in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da taswirar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen dake tsakiya da gabashin Turai
2013-11-27 17:47:30 cri

An kaddamar da shirin Bucharest mai kunshe da tsarin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen dake tsakiya da gabashin Turai a jiya Talata, bayan da shugabannin bangarorin biyu, suka tattaunawa sosai kan dangantakar dake tsakanin su.

An kaddamar da wannan shiri ne a yayin taron tattaunawa da aka gudanar tsakanin shugabannin kasar Sin, da na kasashe 16 dake tsakiya da gabashin Turai, a kuma karkashin shugabancin firaministan kasar Sin Li Keqiang da har yanzu ke ci gaba da ziyarar aiki a kasar Romania, da hadin gwiwar takwaransa na kasar ta Romania.

Wannan shirin hadin gwiwa da aka fitar ba da dadewa ba, ya tabbatar da manufar hadin kai tsakanin kasar Sin da kasashen dake tsakiya da gabashin Turai a nan gaba, inda aka yi cikakkun shirye-shirye kan hakikanan matakan da za a dauka, da batutuwan da za a mayar da hankali a kai a nan gaba. Har illa yau an gabatar da burin da ake fatan cimma, na tabbatar da samun kudin cinikayya, da yawansu zai ninka sau biyu bisa na yanzu a cikin shekaru biyar masu zuwa.

Wani samfurin jirgin kasa mafi sauri da tsayinsa ya kai mita 21 kirar kasar Sin da aka ajiye a zauren majalisar dokokin kasar Romania, ya jawo hankulan shugabanni na kasashen dake tsakiya da gabashin Turai. Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi musu bayanin cewa, muhimman abubuwan more rayuwa, da masana'antun samar da na'urori, su ne ginshiki na samar da moriyar juna, da samun nasara tare tsakanin kasar Sin da sauren kasashe abokan hadin gwiwar ta.

Shirin na "Bucharest" da aka gabatar a yayin taron tattaunawar shugabannin, ya nuna wata taswirar inganta samun bunkasuwa tare, tsakanin Sin da kasashen dake tsakiya da gabashin Turai, ya kuma zayyana hanyar karfafa hadin gwiwar dukkanin sassan. Mista Li ya bayyana cewa,

"Kasar Sin tana son karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasashen dake tsakiya da gabashin Turai ta fuskokin samar da jiragen kasa mafiya sauri, da samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da nukiliya, da gina hanyoyin mota, da tashar ruwa, da kuma inganta fasahohin sadarwa da dai sauransu. Sin na kuma fatan gudanar da manyan ayyuka cikin hanzari, da nufin samun karuwar zuba jari tsakanin bangarorin biyu, tare kuma da jawo bunkasuwar cinikayya."

A hannu guda kuma, Li Keqiang ya jaddada cewa, kasar Sin tana son kara shigo da amfanin gona masu inganci, da sauran kayayyakin da suka dace daga kasashen dake tsakiya da gabashin Turai, kana da samarwa Sinawa damar zuwa wadannan kasashe na Turai don yawon shakatawa, da kuma daukar matakan da suka dace don kyautatawa, a kokarin samar da daidaito a yanayin cinikayya.

A shekarun baya, rashin isassun kudi ya kasance cikas ga farfadowar tattalin arzikin kasashen tsakiya da gabashin Turai. Saboda haka ne, kasar Sin take shirin samar da rancen kudi na musamman, da yawan su ya kai dalar Amurka biliyan 10, don tallafar hadin giwar dake akwai tsakaninta da kasashen. Mista Li ya yi bayyani cewa,

"Muna lale marhabin da halartar hukumomin hada-hadar kudi na kasashen dake tsakiya da gabashin Turai wannan aiki, kuma muna maraba da masana'antun da abin ya shafa, da su sa himma don neman shiga a dama da su. Kasar Sin tana son daddale yarjejeniyoyi tare da dukkanin kasashen, game da musayar kudaden da suke amfani da su a hukumance, da cinikayya da irin wadannan kudade, domin samar da muhalli mai kyau ga masana'antun su wajen zuba jari."

Bugu da kari, wannan shirin hadin gwiwa ya kunshi cewa, kasar Sin, da kasashen dake tsakiya da gabashin Turai, za su hada kai bisa matsayin girmama juna, da tabbatar da daidaito, da tsayawa kan neman cimma moriyar juna, da samun nasarori tare, da neman bunkasuwa tare, da kuma tsayawa kwarai wajen gudanar da hadin kai tsakanin bangarorin biyu, tare da neman cimma ra'ayi guda. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China