Jagorar tawagar hadin gwiwar MDD da hukumar yaki da makamai masu guba ko OPCW Sigrid Kaag, ta jinjinawa abin da ta kira cikakken goyon baya, da mahukuntan kasar Sham suka baiwa tawagarta, yayin aikin lalata makaman kasar masu guba.
Kaag ta bayyana hakan ne ga manema labaru, bayan ta fayyacewa wakilan kwamitin tsaron MDD halin da ake ciki, don gane da yunkurin da ake yi na raba kasar ta Sham da makamai masu guba. Ta ce, tawagar hadin gwiwar ta amfana matuka da ga irin hadin kai da goyon baya da ta samu daga Damascus, matakin da ya ba da damar gudanar da aikin lalata makaman cikin nasara. (Saminu)