in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Syria ta mamaye manyan garuruwan dake yankin karkarar babban birnin kasa
2013-11-09 17:27:36 cri
A 'yan kwanakin da suka gabata ne dai, dakarun sojin gwamnatin kasar Syria suka mamaye sansanonin sojan gamayyar 'yan adawa da ke kusa da lardin Aleppo, na arewacin kasar, da kuma manyan garuruwan da ke wajen babban birnin kasa, lamarin ya janyo matukar asara ga kungiyar dake adawa da gwamnarin kasa.

Wani jami'in rundunar sojan dake wajen birnin Damascus ya bayyana cewa, garuruwan da sojojin gwamantin kasar sun mamaye na da tasiri sosai bisa manyan tsare-tsare, hakan kuma zai ba da matukar taimako ga sojojin gwamnatin wajen cimma nasarar kawar da dukkan kungiyoyin 'yan ta'adda da ke yankunan birnin na Damascus, da kuma shimfida yanayin zaman lafiya da na tsaro a yankin Blackstone.

Har ila yau, bisa labarin da aka samu, an ce, ran 8 ga wata, MDD ta yabawa sosai ga hadin kan da gwamnatin kasar Syria ta nuna ga batun lalata makamai masu guba na kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China