Qin Gang ya bayyana haka ne yayin da ke amsa tambayoyin da manema labarai suka yi masa. Ya kuma bayyana cewa, MDD ta ayyana kungiyar kishin Islama ta gabashin kasar Turkistan a matsayin kungiyar 'yan ta'adda, cikin dogon lokaci da suka gabata, kungiyar ta kai hare-hare da dama a kasar Sin da sauran sassan duniya don cimma mummunan burinta wajen raba jihar Xinjiang daga kasar Sin, hare-haren da suka haddasa mutuwa ko jikkatar mutane da dama tare da kawo asarar dukiyoyi, sabo da haka, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakai masu tsanani wajen murkushe kungiyar.
Qin Gang ya jaddada cewa, ya kamata a yi yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda bisa ka'ida daya, kuma ana bukatar hadin gwiwar kasa da kasa wajen gudanar da wannan aiki, bugu da kari, yaki da kungiyar kishin Islama ta gabashin kasar Turkistan ya kasance wani muhimmin aiki na hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda. (Maryam)