in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rikicin tsakani Masar da Habasha ya kara tsananata
2013-06-21 17:02:40 cri

Dangantakar dake tsakanin kasar Masar da Habasha dangane da gaban kogin Nile ta yi tsami saboda Habasha ta yi shirin kafa wata madatsar ruwa. Abin da ya kawo cece kuce mai tsanani a kasashen dake wannan yanki kan albarkatun ruwa.

An ba da labari cewa, wannan madatsar ruwan da Habasha ta yi shirin gina wa yana kan kogin Blue Nile dake kan iyaka tsakanin Habasha da Sudan, wadda ta kasance muhimmin mataki ne na kasar Habasha a cikin shekaru 25 masu zuwa wadda kuma ta shafi dala biliyan 12. Yawan wutar lantarki da za ta samar zai kai megawatt 6000, hakan ya sa za ta zama na'urar samar da wutar lantarki mafi girma a nahiyar Afrika. Amma wannan aiki zai kawo wasu kasashe dake matakin karshe na wannan kogi illa wajen yin amfani da albarkatun ruwa ciki hadda Masar. Wakilan kasashen Habasha, Masar, Sudan da kuma masanan kasa da kasa kan albarkatun ruwa sun taba kafa wani kwamitin kimantawa a watan Mayu na shekarar 2012 domin kimanta tasiri da madatsar ruwa za ta kawowa wadannan kasashen dake dab da kogin Nile. A farkon watan Yuni na wannan shekara, bayan kwamitin ya gabatarwa Masar wani rahoto, rikicin dake tsakanin Masar da Habasha kan wannan batu ya kara tsananata. Ko da yake, gwamnatin Habasha ta sanar da cewa, wannan aiki ba zai rage yawan albarkatun ruwan da Masar za ta mallaka ba, amma a ganin Masar, Habasha ba ta gabatar da hakikanin bayani kan wannan aiki ba, idan ta kafa ita, yawan ruwan da Masar za ta samu daga kogin Nile zai ragu da kimanin cubic mita biliyan 10 a ko wace shekara, yawan wutar lantarki da madatsar ruwa ta Aswan za ta samar shi ma zai ragu da kashi 18 cikin dari.

Ban da haka, jami'an gwamnatin kasar Masar sun dauki tsattsauran mataki kan wannan batu. Shugaban kasar Mohamed Morsi ya jaddada a gun wani taron da aka yi a ran 3 ga wata kan batun isashen ruwa na kogin Nile cewa, kasar za ta dauki matakai da suka dace domin ba da tabbaci ga isashen ruwa a kasar. A ran 10 ga wata kuwa, firaministan kasar Hisham Qandil ya ba da sanarwa cewa, zai aiko ministan harkokin waje Mohamed Kamel Amr domin ya isa birnin Addis Ababa kan batun madatsar ruwa, tare kuma da jaddada cewa, albarkatun ruwa na da alaka sosai da zaman rayuwar jama'ar kasar. Mai ba da shawara ga shugaban kasar, Ayman Ali, yayin da ya tabo wannan batu ya ce, ya kamata a kiyaye hakkin kasar na yin amfani da albarkatun ruwa. Ban da haka, shugaban jam'iyya dake kan matsayi na biyu a kasar, Younis Makhayoum ya ba da shawarar tura masu aikin leken asiri da su kai hari kan madatsar ruwa. Wadannan zance kuwa ya haifar da damuwa sosai kan yadda wadannan kasashe za su rarraba albarkatun ruwan kogin Nile yadda ya kamata.

A hakika dai, wannan matsala ta kasance ta dau lokaci mai tsawo ana fuskantar ta. Akwai alaka da 'yan mulkin mallaka wadanda suka sa kaimi ga cimma yarjejeniyar rarraba ruwa inda aka samu rashin daidaituwa. Abin ya kara tsananta ne, saboda karuwar mutane da bunkasuwar sha'anin noma da masana'antu a yankin da kogin Nile ke malala.

Kogin Nile ya ratsa kasashe 11, 9 daga cikinsu ne sun cimma wata yarjejeniyar a shekarar 1929 bisa shawarar 'yan mulkin mallaka na kasar Birtaniya, wanda ya baiwa kasar Masar da Sudan hakkin yin amfani da ruwan Nile da farko. Bisa wannan yarjejeniyar, yawan ruwan da Masar da Sudan suke yin amfani da shi a ko wace shekara ya kai cubic mita biliyan 48 da biliyan 4. Ban da haka, yarjejeniyar ta tanade cewa, Masar na da alhakin rarraba ruwan kogin da kuma gina ayyuka a kan kogi ba tare da sanarwa kowa ba, har ma na da ikon kin yarda da wasu ayyuka wadanda a ganinta za su kawo illa gare ta da sauransu. Habasha ba ta shiga wannan yarjejeniya ba.

Ban da haka kuwa, Masar da Sudan sun kulla wata sabuwar yarjejeniya a shekarar 1959 wadda ta tanadi cewa, yawan ruwan da za su yi amfani da su a ko wace shekara ya kai cubic mita biliyan 55.5 da biliyan 18.5. Abin da ya jawo fushin daga sauran kasashe.

Tuni dai, kasar Masar da Sudan sun riga sun gina wasu ayyuka a kan kogin Nile bisa rinjayensu na shimfidar wuri, tattalin arziki, kimiyya da kwadago. Amma, saboda bunkasuwar sauran kasashe, yawan bukatunsu na ruwa ya karu kwarai, hakan ya sa, ake samun rigingimu tsakanin wadannan kasashe. Alal misali namoma da makiyayan Sudan, Sudan ta kudu, Habasha, Kenya su kan samu rikici tsakaninsu domin neman samun albarkatun ruwa. Wannan matsala dake tsakanin Masar da Habasha ya samu tushe daga wadannan rikice-rikice, wadda kuwa ta kara tsananta.

A ganin wasu manazarta, ya kamata Masar, Sudan da Habasha su amince da juna tare kuma da yin shawarwari tsakaninsu ta yadda za su cimma matsaya daya kan rarraba ruwa; da kuma kasashen daban-daban a wannan yanki su kulla wata sabuwar yarjejeniya da ta samu amincewarsu ta yadda za a ba da tabbaci ga moriyarsu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China