131029Habasha_Amina
|
Ministan albarkatun ruwa da makamashi na kasar Habasha Alemayehu Tegenu, ya ce gwamnatin Habasha ta kaddamar da wani tsarin tattalin arziki wanda zai baiwa muhalli kariya, a yunkurin kasar na cimma burinta na kasancewa mai matsakaicin tsarin samar da kudin shiga, tare da rage gurbatar iska kafin shekara ta 2025.
Tegenu, ya bayyana hakan ne yayin bikin rufe taron koli dangane da makamashi na Babban Valley, wato GRVES da aka yi a ran 24 ga watan nan na Oktoba. Bisa wannan tsari na bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, Habasha za ta hada samun bunkasuwar tattalin arziki da kiyaye muhalli tare, baya ga dora muhimmanci kan kyautata fasahar sha'anin noma da kiwon dabbobi, kiyaye da kyautata gandun daji, da kara karfin bunkasa makamashi mai tsafta, ta yadda za a iya cimma bukatun samar da makamashi na gida, da kuma wanda ma za a iya fitarwa zuwa ketare.
Tegenu ya bayyana cewa, Habasha na da makamashi mai tsafta nau'o'i daban daban, ciki hadda damar samar da wutar lantarki ta hanyar ruwa mai karfin megawatt 45,000, da kuma karfin zafi karkashin kasa na megawatt 10,000, har ma da karfin wutar lantarki ta iska mai karfin megawatt miliyan 1.3.
Gwamnatin kasar ta Habasha tana kokarin zuba jari, da kuma sa kaimi ga kafa tashoshin samar da wutar lantarki ta amfani da makamashi mai tsafta, domin cin moriyar amfani da karfinta a fannin makamashi. A sa'i daya kuma, makamashi masu dimbin yawa a wannan kasar na jawo hankali masu zuba jari na kasa da kasa.
An yi bayyanai cewa, ya zuwa yanzu, tashoshin samar da wutar lantarki ta amfani da makamashi mai tsafta da kasar take kafawa, za su samar da wutar lantarki da yawanta ya kai megawatt 8,000, ciki hadda aikin madatsar ruwa ta GERD dake kasar. Yawan wutar lantarki da wannan madatsar ruwa za ta samar zai kai megawatt 6,000, kuma za ta zama daya daga wasu madatsar ruwa mafi girma a nahiyar Afrika. Yanzu haka an kammala kashi 1 bisa 4 na wannan aiki.
Ban da haka, bisa tsarin da gwamnatin kasar ta tsayar, kafin shekarar 2018, yawan wutar lantarki da kasar za ta samar ta karfin ruwa zai kai megawatt 12,500.
A bangare karfin iska kuwa, gwamnatin kasar ta Habasha tana kokarin kafa wasu tasoshin samar da wutar lantarki ta karfin iska. Ciki hadda kamfanin Ashegoda, wanda ba da dadewa ba aka gina shi. An kafa wannan kamfani ne a shekarar 2009, wanda bayan aikin shekaru 4, ake sa ran zai samar da wutar lantarki da yawanta ya kai megawatt 120, inda ake sa ran yawan wutar lantarki da zai samar a shekara guda, ta kai kilowatt miliyan 400 a ko wace sa'a, hakan zai sanya tashar kasancewa mafi girma a wannan fanni a Afrika.
Dadin dadawa, tashar da ake kokarin ginawa yanzu mai suna Adama, na kunshe da matakai na daya da na biyu, wanda ko wannen su, zai samar da wutar lantarki da ta kai megwatt 51.
Haka zalika, a fannin samar da makamashi ta zafin karkashin kasa, kafofin yada labaru sun bayyana cewa, a karshen watan Satumbar bana, wani kamfani mai suna RG, mai kunshe da jarin kasashen Amurka da Iceland, ya kulla kwangila da gwamnatin kasar ta Habasha, kan wani aiki da ya shafi tashar samar da wutar lantarki ta zafin karkashin kasa na Corbetti, wanda zai kashe kudi da yawansu ya kai dala biliyan 4. Wannan fasaha za ta yi aiki da makamashin dake yankin tsaunika masu aman-wuta na Corbetti, dake kudu maso yammacin kasar, domin kafa wata tasha dake iya samar da wutar lantarki har megawatt 1,000. Wannan aiki za a shafe shekaru 8 zuwa 10 ana gudanar da shi, yana kuma da sassa biyu. Bayan kammalarsa, zai zama irin sa mafi girma a nahiyar Afrika.
Ban da haka, amfani da makamashi daga tsirrai ya kasance wani muhimmin mataki, na bunkasa tattalin arziki bisa makamashi mai tsafta. Hakan ya sa kasar ta Habasha, ke kokarin bunkasa wannan aiki. (Amina)