Hukumar hasashen yanayi ta kasar Sin ta tsara shirin ayyukan yaki da gurbatacciyar iska
A ranar 20 ga wata, hukumar hasashen yanayi ta kasar Sin ta bayyana cewa, kwanan baya, hukumar ta bayar da shirin ayyukan yaki da gurbata cciyar iska, inda ya bayyana cewa, ya zuwa shekarar 2015, hukumar hasashen yanayi da hukumar kiyaye muhalli ta kasar za su aiwatar da shirin ko-ta-kwana wajen yaki da gurbatar yanayi a dukkan larduna da biranen kasar.
Bisa wannan shiri, an ce, ya zuwa shekarar 2015, sassan kula da hasashen yanayi na larduna da biranen kasar za su dauki matakai don kyautata ingancin iska, haka kuma, za a dauki matakai wajen canja yanayi, yayin da aka samu gurbatar yanayi sosai, kuma za a dauki matakai don yaki da babban hazo, da kyautata ingancin iska.(Bako)