in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka da Faransa na fatan samun tabbacin Iran kan batun nukiliyarta
2013-11-14 10:13:56 cri

Shugaba Barack Obama na Amurka, da takwaransa na Faransa Francois Hollande, na ci gaba da daukar matakan ganin kasar Iran ta ba da tabbaci ga shirin dakatar da duk wani yunkuri na kera makaman kare dangi.

A ranar Laraba ne dai fadar shugaban kasar Faransa, ta fidda wata sanarwa dake bayyana burin shuwagabannin biyu, bayan tattaunawar da suka gudanar ta wayar tarho.

Sanarwar ta kuma rawaito shuwagabannin biyu na dorawa Iran din alhakin samun nasarar da ake fata, muddin dai mahukuntanta, suka amince da kiraye-kirayen da ake musu kan wannan batu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China