Shugaban kasar Cote d'Ivoire, Alassane Ouattara kuma shugaban kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS a wannan karo ya bayyana mutakar bacin ransa tare da yin allawadai da kisan da wasu mutane dauke da makamai suka yi kan 'yan jaridar Faransa biyu a kasar Mali a yayin da suke cikin aikinsu bayan sun sace su a ranar Asabar a Kidal dake arewacin kasar Mali.
Ma'aikatan rediyon kasar Faransa RFI sun hada da Ghislaine Dupont, mai shekaru 57 da Claude Verlon, mai shekaru 58 da mutanen suka sace a ranar Asabar da misalin karfe daya na rana, agogon wurin a bakin kofar gidan Ambery Ag Rhissa, wakilin kungiyar 'yan tawayen Abzinawa MNLA bayan sun kare hira da shi kafin a gano gawawwakinsu in sa'o'i kadan.
A cikin sanarwar ta ranar Litinin, shugaban kungiyar ECOWAS ya bayyana bacin rai tare da yin allawadai da wannan kisa.
Mutuwar wadannan 'yan jarida biyu ta razana miliyoyin mutanen Afrika tare kuma da tura iyalin mamatan cikin damuwa sosai, in ji Alassane Ouattara tare da jaddada cewa, ECOWAS za ta cigaba da aiki domin maido da zaman lafiya da tsaro a kasar Mali, musammun ma a yankin Kidal. (Maman Ada)