Sharhin ya bayyana cewa, a shekaru fiye da 30 da aka bude kofa da yin kwaskwarima a kasar Sin, an samu bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri, har yanzu haka yawan tattalin arzikin kasar ya kai matsayi na biyu a duniya, kuma hakan ya kyautata rayuwar jama'ar kasar. Don haka idan ana son kiyaye bunkasuwar tattalin arzikin kasar yadda ya kamata, dole sai a maida babbar moriyar jama'a a gaban kome, da yin amfani da kimiyya da fasaha, da kuma samun bunkasuwa ba tare da samun haddura ba. Sharhin ya ce, ya kamata a yi amfani da nasarorin da aka samu wajen bunkasa tattalin arziki ta fuskar amfanar da jama'a, ta yadda irin wannan bunkasuwa za ta biya bukatun jama'a tare da kasancewa cikin dorewa.
Ban da wannan kuma, sharhin ya nuna cewa, kamata ya yi jami'an kasar su yi kokarin samun bunkasuwa mai inganci da kara amfana da jama'a, tare da maida kiyaye tsaron lafiyar jama'a a yayin aiki a gaban komai, da kuma yin amfani da aikin kiyaye haddura yayin aiki wajen canja tsarin tattalin arzikin kasar. (Zainab)