A ganin wakilai daga bangaren soja masu halartar taron, kara yawan kudin da za a kashe a fannin tsaron kasa zai tabbatar da cimma burin sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin na samun nasara a yaki. Yawan kudin da aka kashe a fannin tsaron kasa bai taka kara ya karya ba idan aka kwatanta da yawan kudin da aka kashe domin raya tattalin arziki. Wakilin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin kuma manazarci a kwalejin kimiyyar aikin soja na kasar Chen Zhou ya bayyana cewa, ana kokari domin yawan kudin da za a kashe a fannin tsaron kasa ya dace da matakin bunkasuwar tattalin arzikin kasar.
Mataimakin shugaban kwalejin nazarin ilmin aikin soja kuma memban majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Liu Jian ya bayyana a ranar 5 ga wata cewa, yawan kudin da aka kashe a fannin nazarin fasahohin tsaron kasa kashi daya ne cikin kashi arba'in kawai bisa na kasar Amurka. Ya ce, akwai gibi sosai a tsakanin Sin da sauran manyan kasashen duniya a bangaren kayayyakin aikin soja. (Zainab)