Kawo yanzu dai, ba a tantance ko suwaye wannan hari ya ritsa da su ba.
Bisa labarin da aka samu, an ce, an samu fashewar boma-boman ne a yankin kudancin birnin Beirut, inda kungiyar Hizbollah take da karfi.
Ban da ofisoshin jakadanci na kasar Iran da na sauran kasashe, akwai kuma gidajen ma'aikatansu, da gidan telebijin na Mesbah mallakar kungiyar Hizbollah da dukkaninsu ke wannan yanki.
Jim kadan da aukuwar wannan lamari, wani jigo a kungiyar Al-Qaeda mai suna Abdullah Azzam, ya sanar da tayar da wannan fashewar boma-bomai a shafin Internet na sada zumunta. Jami'in kungiyar ya bayyana cewa, an kai wannan hari ne, domin matsawa Hizbollah lamba ta janye jiki daga Siriya.
Kasashen duniya da ragowar masu ruwa da tsaki sun mayar da martani game da fashewar boma-bomai. Inda kwamitin sulhu na M.D.D., da sakatare janar na M.D.D., da kasashen Iran, da Amurka, da Siriya suka ba da sanarwa daya bayan daya, dake Allah wadai da aukuwar wannan hari.
A cewar kwamitin sulhu na M.D.D., ya zama dole a gurfanar da masu hannu cikin wannan hari gaban kuliya, a sa'i daya kuma, an sake jaddada nauyin dake wuyan gwamnatin kasar, na daukar matakan kiyaye ofisoshin jakadancin kasashen duniya, don magance kai musu hari. (Bako)