Ana sa ran wakilai daga kasashen Amurka, da Rasha, da Sin, da Faransa, da Birtaniya, da Jamus, da kuma Iran za su ci gaba da kokarin daddale yarjejeniya kan wannan batu a wannan karo.
A wannan rana, bayan da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu suka kammala shawarwari tsakaninsu, shugaba Putin ya fada wa kafofin yada labaru cewa, Rasha na farin ciki da ganin an kaddamar da taron tattaunawar na wannan lokaci.
Har ila yau wani jami'in diplomasiyyar kasar Amurka ya bayyana a wannan rana cewa, sai a daddale yarjejeniya daga dukkan fannoni game da batun nukiliyar kasar ta Iran kawai, kasashen yammacin duniya za su iya soke takunkumin da suka kakabawa kasar.
Shi ma a jawabin sa na wannan rana, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Li Baodong, ya bayyana cewa, an gudanar da shawarwari a karon da ya gabata cikin tsanaki, kuma bangarori daban daban, sun bayyana aniyyar su, ta warware batun nukiliyar kasar Iran ta hanyar yin shawarwari a siyasance.
Yace an riga an cimma matsaya guda a wasu muhimman fannoni, kuma dukkan sharuddan da aka cimma sun zamo wani muhimmin harsashi ga ci gaba da yin shawarwarin a wannan karo.(Bako)