in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron shugabanni na fadar Elysee zai mai da hankali kan tsaro da bunkasuwa a Afirka
2013-11-22 10:43:38 cri

Shugaban kasar Faransa Mista Francois Hollande ya sanar a ranar Alhamis 21 ga wata da cewa, shugabanni fiye da 40 da za su zo daga kasashen Afirka za su yi taro a Fadar Elysee na shugaban kasar daga ranar 6 zuwa 7 ga watan Disamba na bana, inda za a tattauna kan tsaron a nahiyar, da tinkarar sauyawar yanayin duniya da bunkasuwar tattalin arziki da dai sauransu.

Bayan ganawarsa da takwaransa na kasar Guinea Alpha Conde a wannan rana a fadar Elysee, Mista Hollande ya shaida manema labaru cewa, shugabannin da kasar Faransa ta gayyace su, za su zo ne daga kasashen Afirka masu amfani da harsunan Faransanci, da Turanci, da kuma Portugal.

Kafofin watsa labarai sun fadi cewa, taron shugabanni na fadar Elysee zai tattauna kan yaki da ta'addanci, da tinkarar 'yan fshin teku da tabbatar da tsaro a iyakokin kasashen Afirka, da kafa wata rundunar sojojin daukar matakan gaggawa, da inganta dangantakar zumunci a fannin tattalin arziki da raya kasa da dai sauransu.

Mista Hollande ya sanar tun a watan Mayu a birnin Addis Ababa babban birnin kasar Habasha cewa, taron shugabanni da za a kira a fadar Elysee a watan Disamba zai tattauna yanayin tsaro da zaman lafiya a Afirka.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China