in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron tattauanwa na hadin gwiwar Sin da Afirka karo na hudu a birnin Hainan na Sin
2013-11-20 21:34:33 cri
Yau Laraba 20 ga wata ne aka yi taron tattaunawa na hadin gwiwar Sin da Afirka karo na hudu a birnin Hainan na kasar Sin, inda mahalarta taron suka bayyana cewa, matsayin dangantakar kasashen Sin da Afirka na ci gaba da dagawa cikin harkokin wajen kasashen Sin da Afirka, kuma moriyar iri daya da kasashen Sin da Afirka suke son cimmawa na ci gaba da karuwa, sabo da haka, ana fatan alheri ga bunkasuwar dangantakar kasashen Sin da Afirka.

Babban taken taro na wannan karo shi ne "hadin gwiwa da cimma moriyar juna", mutane sama da dari hudu da suka hada da jami'an gwamnati, shugabannin kamfanoni, masana na fannoni daban daban ne suka halarci bikin bude taron, kuma jakadu na kasashen Afirka sama da 40 sun halarci bikin.

Tsohon shugaban kungiyar jadakun kasar Sin, kuma mai jagorantar taron tattaunawa na hadin gwiwar Sin da Afirka Ji Peiding ya bayyana a yayin taron cewa, hadin gwiwar tattalin arzikin kasar Sin da kasashen Afirka na ci gaba da bunkasa cikin yanayi mai kyau, kuma bunkasuwar Sin da Afirka za ta ci gaba da tallafawa juna. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China