Mataimakin shugaban kasar Afirka ta kudu ya yi maraba da kamfanonin Sin da su zuba jari a kasar
A ranar 28 ga wata a nan birnin Beijing, mataimakin shugaban kasar Afirka ta kudu Motlanthe ya bayyana cewa, kasarsa da kasar Sin manyan abokan hadin gwiwa ne, kuma kasar Afirka ta kudu tana maraba da kamfanonin Sin da su zuba jari a kasar a fannonin makamashin da ake iya sake sarrafa shi a kasar, ma'adinai, hada-hadar kudi, kere-kere, gina hanyoyin jiragen kasa da dai sauransu.
Motlanthe ya bayyana hakan ne a gun bikin bude taro na 5 na kwamitin kula da dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka ta kudu. Kana ya yi fatan za a shigar da hadin gwiwar kimiyya da fasaha da kuma ilmi cikin abubuwan da za a tattauna a gun taron. (Zainab)