Kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta bukaci taimakon gaggawa daga kasashen duniya ga ayyukan kiyaye zaman lafiya a kasar Afrika ta Tsakiya CAR, kamar yadda shugabar kungiyar Nkosazana Dlamini Zuma ta yi kiran a wani ganawarta da Babacar Gaye, wakili na musamman na magatakardar MDD a kasar Afrikan ta Tsakiya kuma shugaban ofishin hadin gwiwwa na MDD BINUCA.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Laraban nan 9 ga wata, an ce, madam Nkosazana Zuma ta yi kiran da a ba da agajin gaggawa ne daga sauran kasashen duniya domin samar da gudummuwar da ya kamata ga ayyukan kiyaye zaman lafiya cikin hanzari, dalilin halin tsaro da jin kai da ake fuskanta a yanzu haka a kasar.
Madam Zuma har ila yau ta jaddada bukatar dake akwai na amincewa da shawarar kwamitin tsaro na MDD wanda ya goyi bayan a tura dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar da hadin gwiwwar dakarun kasar ta Afrika ta Tsakiya domin share fage ga shirin majalissar na ba da gudummuwa ga rundunar a karkashin shirin hadin gwiwwa dake tsakanin AU da MDD. (Fatimah)