in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya bukaci CAR da ta aiwatar da yarjejeniyar mika mulki
2013-10-11 10:15:12 cri

Kwamitin tsaro na MDD a ranar Alhamis din nan ya yi kira ga kasar Afrika ta Tsakiya CAR da ta aiwatar da ayyukan shirin mika mulki.

A cikin wata shawarar da aka amince, kwamitin ya bukaci dukkan bangarorin da abin ya shafa a kasar da su mutunta yarjejeniyar siyasa da aka rattataba hannu wannan shekarar wadda ta samar da tsarin warware rikicin siyasar da ake fuskanta cikin ruwan sanyi a kasar.

Kwamitin ya kuma bukaci kasar ta Afrika ta Tsakiya da ta yi saurin aiwatar da yarjejeniyar tare da shirya babban zabe a bayyane kuma cikin adalci nan da watanni 18 bayan fara shirin mika mulki da aka yi a ranar 18 ga watan Agusta.

Shi dai kwamitin tsaron mai mambobi 15 ya kuma yi kira ga kungiyar 'yan adawar nan ta Seleka da sauran kungiyoyi masu dauke da makamai da su jinginar da makaman domin a yi aiki tare da su a shirin ajiye makamai da dakatar da duk wani shiri akasin haka.

Dangane da kara karfin ofishin majalissar na samar da zaman lafiya a kasar, kwamitin ya amince da cewa, ofishin ya ba da goyon bayan da ya kamata wajen aiwatar da shirin, hana fadace fadace da ake fuskanta da ba da taimako na jin kai tare da tabbatar da tsaro. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China