in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci hambararren shugaban CAR da ya shiga taron tattaunawa
2013-11-13 10:21:44 cri

Kakakin fadar gwamnatin kasar Afirka ta tsakiya CAR Guy Simplice Kodegue, ya bayyana aniyar gwamnatin kasar mai ci, ta shigar hambararren shugaban kasar Francois Bozize, taron tattaunawar da ake fata zai ba da damar tabbatar da sulhu a fadin kasar.

Da yake bayyana hakan ta wayar tarho ga kamfanin dillancin labarum kasar Sin Xinhua, Kodegue ya ce, duk da kiraye-kirayen da mahukuntan kasar ke yi na shigar tsagin tsohuwar gwamnatin cikin shirin tabbatar da sulhun, a hannu guda akwai shakkun shigar tsohon shugaban kasar wannan tattaunawa. Hakan kuwa, a cewarsa, baya rasa nasaba da sammacen cafke shi da hukumar shari'ar kasar ta fitar, bisa zargin sa da aikata laifin kisan kiyashi a kasar.

Har ila yau, gwamnatin kasar mai ci na zargin sa da kitsa shirin wargaza gwamnati, ta hanyar daukar nauyin mayakan sa kai a mahaifarsa dake yankin arewa maso yammacin kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China