Lavrov ya jaddada cewa, a halin yanzu kasashe shida da batun nukiliya na kasar Iran ya shafa suna kokarin neman shirin warware batun, kana sabbin shugabannin kasar Iran suna da ra'ayi iri daya game da wannan. Sabo da haka, bangarori daban daban da abin ya shafa suna da damar samun ci gaba wajen warware batun. Kana Lavrov ya ce, kasar Iran ta nanata cewa, ta shirya warware dukkan matsalolin da hukumar IAEA ta gabatar a mataki mataki a cikin shekara guda don kawar da dalilin sanya takunkumi kan kasar Iran.
Ministan harkokin waje na kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya ce, za a ci gaba da yin shawarwari kan batun nukiliya na Iran a ranar 20 ga wata, kuma yana fatan bangarori daban daban da abin ya shafa za su cimma wata yarjejeniya. (Zainab)