Taron ya kuma amince da bukatar kira ga mahukuntan kasar Sudan, da kada su sanya takunkumin hana safarar man makwafciyarta Sudan ta Kudu, tare da amincewa da gudanar da ayyukan da abin ya shafa yadda ya kamata.
Dadin dadawa, kwamitin sulhu ya yi kira ga bangarorin da abin ya shafa, da kada su yi amfani da karfi kan fararen hula, ya kuma kamata su ba da damar shigar masu aikin ceto, da kuma kayayyakin agaji yadda ya kamata, a kokarin da ake yi na taimakawa fararen hula a sassan kasashen biyu.(Fatima)