in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bayyana rashin jin dadinta don gane da kazawar kwamitin tsaron MDD game da batun jinkirta shari'ar shugaban Kenya
2013-11-16 16:40:11 cri
Kasar Sin ta bayyana rashin gamsuwa, da yadda kudirin jinkirta tuhumar da kotun ICC ke wa shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya gaza samun cikakken goyon baya a zauren kwamitin tsaron MDD.

Zaunannen wakilin kasar ta Sin a MDD Liu Jieyi ne ya bayyana haka, jim kadan da kammala kuri'ar da aka kada kan kudirin, wanda ke bukatar kotun hukunta manyan laifukan ta ICC, da ta dade shari'ar da ta fara gudanarwa kan shugaban kasar ta Kenya.

Sakamakon kuri'ar da aka kada kan wannan kuduri, ya nuna cewa, cikin mambobin kwamitin 15, 7 ne suka jefa kuri'un goyon baya, ciki had da Sin da Rasha, yayin da kuma ragowar kasashe 8, da suka hada da Birtaniya, da Faransa da Amurka, suka ki jefa nasu kuri'u. Wanda hakan ya nuna gazawar da kudurin ya yi, na samun amincewar kwamitin na tsaro.

Da yake karin haske don gane da lamarin, Mr. Liu ya ce, batun neman dage karar shugaban kasar ta Kenya, ya wuce bukatar kasarsa kadai, a cewarsa wannan bukata ce ta dukkanin kasashen Afirka, wadda kuma ke matukar bukatar a ba ta kulawar da ta dace.

Daga nan sai ya yaba wa mahukuntan kasar ta Kenya, bisa kokarinsu na daidaita sashen shari'ar kasar, da habaka warware takaddamar siyasa, da samar da daidaito tsakanin al'ummun kasar. Wakilin kasar ta Sin ya kuma yabi irin ci-gaba da kasar ke samu ta fuskar yaki da ayyukan ta'addanci, matakin da ya ce, ya yi matukar tasiri ga wanzuwar yanayin zaman lafiya da tsaron yankin Gabashin nahiyar Afirka baki daya.

Bisa wannan ci-gaba da kasar ke samu ne, Mr. Liu ke ganin ya dace matuka kasashen duniya su bai wa mahukuntanta damar gudanar da mulkin kai bisa doron doka, ciki had da batun inganta tsaron kasa, da ma tabbatar da kwanciyar hankali a yankin baki daya. Ya ce, a kokarin da daukacin hukumomin shari'a na kasa da kasa ke yi, na tabbatar gudanar da ayyukan da doka ta tanada, kamata ya yi a yi la'akari, tare da martaba ikon 'yancin mulkin daidaikun kasashe, da al'adunsu, da kuma ikon cin gashin kai.

Haka zalika, jakadan kasar ta Sin ya jaddada matsayin kasar Sin, na amincewa da tabbatar wancan kuduri, na dage shari'ar shugaba Kenyatta, yana mai cewa, dalilan da kasahen nahiyar ta Afirka, karkashin kungiyar AU suka gabatar na da madogara mai karfi. Liu na ganin kasashen Afirkan ne suka fi kowa sanin bukatunsu.

"Bukatar kasashen ba ta wuce kokarin tabbatar da tsaro ba, da wanzar da managarcin yanayin zaman lafiya, tare da yaki da ta'addanci. Abin da kawai suke bukata shi ne, bai wa jagororin kasar ta Kenya, da al'ummarsu suka zaba martabawar da ta dace." a kalaman zaunannen wakilin kasar ta Sin a MDD.

Da yake nanata aniyar kasar Sin game da ci gaba da goyon bayan bukatun kasar ta Kenya, da ma sauran kasashen nahiyar ta Afirka, don gane da lalubo hanyar warware wannan batu, Mr. Liu ya yi fatan kwamitin tsaron zai yi nazari mai zurfi, tare da sake la'akari ga wannan bukata ta kungiyar AU, wadda ke bukatar dage waccan kara zuwa akalla shekara Guda.

Idan dai ba'a manta ba, a ranar 31 ga watan Oktobar da ya shude ne, kotun ICC ta dage sauraron shari'ar shugaba Kenyatta, da mataimakinsa William Ruto, zuwa ranar 5 ga watan Fabrairun shekara mai zuwa.

Ana dai zargin jagororin kasar ta Kenya ne da aikata laifuka yaki, ciki hadda rura wutar rikici, lamarin da ya haddasa kisan fararen hula da dama, da tsunduma dubban al'ummar kasar cikin mawuyacin hali, biyowa bayan rikicin siyasar kasar da ya barke, bayan kammalar babban zaben kasar na shekarar 2007.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China