in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bai dace a gurfanar da shuwagabanni masu ci gaban kuliya ba, in ji shugaba Zuma
2013-11-07 09:54:11 cri

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma, ya jaddada cewa, sam bai dace a gurfanar da shuwagabannin kasashen Afirka masu ci gaban wata kotun hukunta laifuka yayin da suke kan karagar mulki ba.

Shugaba Zuma wanda ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin wakilan majalisassar dokokin kasarsa, don gane da batun gurfanar da wasu shugabannin Afirka gaban kotun hukunta manyan laifuka ta ICC, ya kara da cewa, abin gudu shi ne samar da gurbin shugabanci a irin wadannan kasashe, da shugabannin suke fuskantar tuhuma.

A yanzu haka dai kotun ta ICC na da burin gudanar da shari'a ga shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, da mataimakinsa William Ruto, bisa zarginsu da ake yi na rura wutar fitina, yayin babban zaben kasar da ya gudana a shekara ta 2007, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane sama da 1,000.

Wannan mataki da ICCn ke niyyar dauka ya sanya wasu daga shugabannin kasashen Afirkan yin barazanar janye goyon bayansu gare ta, a hannu guda kuma kungiyar AU ta yi kira da kwamitin tsaron MDD, da ya umarci ICCn ta dakatar da shari'ar shugaba Kenyatta, da mataimakinsa har izuwa karshen wa'adin mulkinsu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China