in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan kasar Kenya na fatan karfafa dankantaka da kasar Sin
2013-08-14 10:01:22 cri

Rahotanni daga Kenya na cewa, shugaban kasar Uhuru Kenyatta, zai gudanar da wata ziyarar aiki ta kwanaki 5 a nan kasar Sin, tun daga ranar 18 zuwa 23 ga watan nan na Agusta da muke ciki.

Wannan ziyara, a cewar ministar ma'aikatar lura da harkokin waje da cinikayyar kasashen ketare Amina Mohamed, za ta baiwa shugaba Kenyatta zarafin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi hadin gwiwa, da dangantakar diplomasiyya da shugaba Xi Jinping, da ma ragowar kusosin gwamnatin kasar ta Sin.

Har ila yau, ana sa ran wannan ganawa tsakanin shuwagabannin biyu, za ta ba da damar zakulo hanyoyin habaka tattalin arzikin kasashen biyu, tare da zurfafa hadin gwiwa a sauran fannonin ci gaba, ciki hadda batun inganta kayayyakin more rayuwa, da yawon shakatawa, tsaro da kuma wanzar da zaman lafiya.

Ziyarar da shugaban kasar Kenya zai kawo kasar Sin a wannan karo za ta dace, da lokacin da ake bikin tunawa da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu shekaru 50 da suka gabata. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China