Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC, ta dage zaman sauraron tuhumar da akewa shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya, zuwa ranar 5 ga watan Fabrairun shekarar badi.
Ana dai tuhumar Mr. Kenyatta, da mataimakinsa William Ruto, da kuma wani 'dan jarida mai suna Joshua Sang ne, da laifin cin zarafin bil Adama, da gwada karfin tuwa kan fararen hula, a lokacin tashin hankalin bayan zaben kasar na shekara 2007 zuwa 2008.
Lauyoyin Mr. Kenyatta a ranar 24 ga watan da ya gabata sun mika bukatar jinkirta soma shari'ar da ake burin farawa ranar 12 ga watan Nuwambar nan, bukatar da kotun ta amince da ita.
Wannan shari'a dai da shugaba Kenyatta ke fuskanta, ta biyo bayan zaben kasar na shekarar 2007 ne, wanda tsohon shugaba Mwai Kibaki, da babban 'dan adawarsa Raila Odinga suka shiga, matakin da ya haddasa yamutsi da tashe-tashen hankula na tsahon watanni biyu, lamarin da kuma ya janyo mutane sama da 500,000 suka kauracewa gidajensu. (Saminu)