in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban Kenya ya bukaci ICC da ta dakatar da shari'arta domin jiran kwamitin tsaron MDD
2013-10-16 12:43:54 cri

Mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto ya yi kira a ranar Talata ga kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya ICC da ta dakatar da yin shari'a kansa da shugaban kasar Uhuru Kenyatta har jin ta bakin kwamitin tsaro na MDD.

Mista Ruto dake a yanzu haka a Pays-Bas na zargin ICC da kasawa a kan aikinta na yin bincike kan zarge-zargen da ake masu, ko da yake ya dauki niyyar baiwa kotun ta MDD hadin kai, a cewar wata sanarwa ta ofishinsa dake birnin Nairobi.

'Ko shakka babu, hanyar da ake bi na zargin mu, akwai matakin magudi a ciki, bai wa masu shaidu kudi bisa yunkurinsu da su zarge mu da laifi, hakan ya kasance abin yin allawadai. Shugaba Uhuru Kenyatta da ni kaina za mu cigaba da ba da hadin kai ga ICC.' in ji mista Ruto.

Mista Ruto ya yi wannan furuci bayan wata bukatar da ya gabatar wa kungiyar tarayyar Afrika da ta yi kira ga kwamitin tsaro na MDD da ya sanya baki, ta yadda za'a gusa wannan harka daga wajen ICC.

Taron shugabannin kasashen kungiyar AU ya tsai da wa'adi da ya kamata ICC da kwamitin tsaro na MDD su girmama kafin fara shari'ar mista Kenyatta a ranar 12 ga watan Nuwamba.

AU ta bukaci kasar Kenya da ta aika da wasika zuwa ga kwamitin tsaro na MDD domin neman dage batun, kamar yadda kuduri mai lambar 16 na yarjejeniyar Rome ya tanada kan tuhumar da ake wa shugaban kasar Kenya da mataimakinsa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China