in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar shugaban kasar Sin a Kongo Brazzaville za ta zurfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu
2013-03-22 17:32:59 cri






A yau ne sabon shugaban kasar Sin Mr Xi Jinping ya fara ziyarar aiki ta farko a wa'adin mulkinsa, zuwa wasu kasashe daga yau Juma'a 22 ga wata, ciki hadda Rasha, da Tanzaniya, da Afrika ta kudu, da kuma Kongo Brazzaville.

Shugaba Xi ya kasance shugaban kasar Sin na farko da zai kai ziyara a kasar Kongo Brazzaville tun bayan kafuwar Jamhuriyyar Jama'ar kasar ta Sin. Jakadan kasar Kongo Brazzaville dake kasar Sin Mr Daniel Owassa yayin zantawa da wakilinmu, ya bayyana cewa ziyarar da Mr Xi zai gudanar za ta zurfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Yayin da Daniel Owassa yake tattaunawa da wakilinmu, ya waiwayi ci gaban da kasar Sin, da Kongo Brazzaville suka samu wajen raya dangantakar dake tsakaninsu. Yana mai jaddada cewa, yadda aka zabi Kongo Brazzaville ta zama daya daga cikin kasashen da da Xi Jinping zai gudananr da ziyara bayan ya kama aiki a matsayin shugaban kasar Sin, ya sheda dankon zumunci dake tsakanin kasashen biyu. Ya ce:

"Sin da Kongo Brazzaville abokan juna ne dake da zumunci mai karfi a tsakaninsu. Ziyarar Xi zai kasance ta farko da shugaban kasar Sin ke yi a kasar, abin da ya bayyana dangantakar kut da kut dake tsakaninsu, za kuma ta zama wani sako dake bayyana ci gaban da suka samu wajen raya dangantakar bangarorin biyu. Ina farin ciki kwarai da gaske, da shaida wannan dankon zumunci dake tsakanin kasashen biyu."

Bana ta cika shekaru 49 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da Kongo Brazzaville. A cikin wadannan shekaru kasashen biyu sun samu ci gaba sosai wajen yin hadin gwiwa a fannoni daban-daban. Ko da yake, duk da wasu matsaloli da aka fuskanta amma bangarorin biyu na mai da juna a matsayin shakikan kawaye. Game da wannan batun, Daniel Owassa ya bayyana cewa:

"Akwai abokantaka ta fanni biyu, da farko, samun ci gaba tare, sa'an nan kuwa tinkarar kalubaloli tare. Sin da Kongo Brazzaville sun kasance a rukunin abokantaka na biyu, kasashen biyu sun kulla abokantaka tuni a lokacin da kasar Sin ke fama da koma baya, a waccan lokaci babu kasashe da yawa da suka kulla dangantakar kut da kut da kasar Sin.

Idan mun waiwayi baya, kasashen biyu sun tinkari kalubaloli da mawuyacin hali tare har tsawon lokaci, har ila yau kuwa, kasashen biyu sun kiyaye dangantakar dake tsakaninsu, dadin dadawa, kasashen biyu za su ci gaba da yin kokari wajen zurfafa wannan dangantaka."

Kamar yadda Daniel Owassa yake bayyanawa, Sin da Kongo Brazzaville na da dangantaka mai karfi, akwai batutuwa biyu da Sinawa ba su iya mantawa da su ba. Na farko, bayan da girgizar kasa mai tsanani ta abkuwa a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan ta kasar Sin a shekarar 2008, duk da rikice-rikice da koma bayan tattalin arziki da aka fuskanta a Kongo Brazzaville a wancan lokaci, kasar ta samar da gudummawar dala miliyan 1 ga Wenchuan. Na biyu kuwa, a yayin da gundumar Yushu ta jihar Tibet mai cin gashin kanta ta yi fama da girgizar kasa mai tsanani a shekarar 2010, Kongo Brazzaville ta sake ba da taimako wajen gina wata makaranta a wurin, ta yadda kananan yara za su iya ci gaba da karatu. Wadannan abubuwa biyu sun shaida zumunci mai inganci tsakanin kasashen biyu.

Bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashe biyu, ba ta rasa nasaba da harkokin cinikayya dake tsakaninsu. Bisa kidddigar da hukumar kwastan ta kasar Sin ta yi, an ce, a cikin shekarar 2011 yawan kudin ciniki a tsakanin kasashen biyu ya kai fiye da dala biliyan 5.1, wanda hakan ya kai wani sabon matsayi a tarihi, har ma ya sa kasar ta Kongo Brazzaville ta kai ga matsayi na biyu, daga cikin kasashe 24 na tsakiya da yammacin Afrika, da suke yin ciniki da kasar Sin, haka kuma matsayin ya kai na bakwai, bisa na dukkanin kasashen Afrika.

Ban da hadin kai a bangaren ciniki, Daniel Owassa yana dora muhimmanci sosai kan musayar al'adu da cudanyar jama'ar tsakanin kasashen biyu, a ganinsa, haka ne jama'ar kasashen biyu za su iya kara fahimtar juna, ta yadda za a karfafa dankon zummunci tsakanin kasashen biyu. Game da wannan batu, Daniel Owassa ya ce:

"Taron ministoci karo na biyar na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika, ya sa kaimi ga ci gaban hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika haka kuma an tattauna batun kafa kwalejin Confucius a Kongo Brazzaville. Wani batu ma na daban da muke mai da hankali a kansa, shi ne kara gude hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye tsakanin Sin da nahiyar Afrika, ta yadda za a kara cudanyar jama'ar sassan biyu."

Kasar Sin tana mai da muhimmanci kan raya dangantakar dake tsakaninta da kasashen Afrika ciki hadda Kongo Brazzaville. Sabuwar gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da zurfafa hadin kai tsakaninta da kasashen Afrika a fannoni tattalin arziki, da ciniki, da siyasa da sauransu, tare da karfafa mu'ammala tsakanin jama'ar bangarorin biyu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China