Kasar Syria ta gabatar da takardar farko ta shirin makamai masu guba, da ke kunshe da shirinta na lalata makamai masu guba, in ji kungiyar hana yaduwar makamai masu guba (OPCW) a ranar Lahadi a cikin wata sanarwa.
Kasar Syria ta gabatarwa OPCW takardar sanarwar farko dake kunshe da jadawalinta na makamai masu guba, in ji wannan hukuma, tare da karin cewa, kundin na kunshe da cikakakken shirin kasar na lalata makamai masu guba da ya kamata kwamitin zartaswa na OPCW ya dauke shi da muhimmanci. Kasar Syria ta bullo da shirin a daidai lokacin da kwamitin zartaswa na OPCW ya tsai da a cikin matakinsa na ranar 27 ga watan Satumban shekarar 2013, inda ake kira ga kasar ta Syria da ta gabatar da takardar bayanai gaba daya kafin ranar 27 ga watan Oktoban shekarar 2014.
Wadannan bayanai suna kasancewa tushen dake dogaro kan shirye-shiryen da aka aiwatar domin lalata makamai masu guba gaba daya da kuma binciken makamai masu guba da wuraren da aka sanar, in ji wannan kundi. (Maman Ada)