Wakilin musamman na hadin gwiwar MDD, da kungiyar tarayyar Larabawa kan batun kasar Sham Lakdar Barahimi, ya ce, taron da kasashen Amurka, da Rasha, da MDD suka gudanar ya gaza cimma matsaya kan ainihin lokacin gudanar da taron Geneva karo na biyu.
Brahimi wanda ya bayyana hakan a ranar Talata 5 ga wata, ya kara da cewa, suna iyakacin kokarin ganin an gudanar da wannan taro, nan da karshen shekarar nan. Ya ce, bambancin wannan taro, da makamancinsa da aka gudanar a watan Yunin bara shi ne, a wannan karo, ana fatan daukacin masu ruwa da tsaki, ciki hadda al'ummar Sham, da tsagin gwamnati, da ma na 'yan adawa za su halarci taron, ko da yake, a cewarsa, kawo yanzu 'yan adawar kasar ta Sham ba su kai ga kimtsawa domin shiga tattaunawar ba.
Don gane da inda aka kwana kuwa, Brahimi ya ce, an tsai da ran 25 ga watan nan na Nuwamba, domin sake zaman duba yiwuwar sanya ranar taron na Geneva karo na biyu, matakin da zai baiwa 'yan adawar kasar ta Sham damar sake shiryawa, domin fuskantar taron na Geneva. (Saminu)