Hukumar wasannin motsa jikin kasar Najeriya da ofishin ministan wasannin motsa jikin kasar Kamaru sun kaddamar tun ranar Litinin da wani shirin karfafa hadin gwiwa da bunkasa dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Darekta janar na hukumar Najeriya, Gbenga Elegbeleye ya sanar da wannan mataki a cikin jawabinsa na bude taron kwararru kan hadin gwiwar wasannin motsa jiki tsakanin Najeriya da Kamaru da ke gudanarwa a birnin Abujan Najeriya har zuwa ranar 13 ga watan Nuwamba.
Zaman taron dai ya biyo bayan tattaunawa tsakanin babban hukumar Najeriya da ma'aikatar wasannin motsa jiki ta Kamaru kan aiwatar da yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma, in ji mista Elegbeleye.
Haka kuma jami'in ya bukaci kwararrun da su yi binciken bullo da dabarun da suka dace bisa misalin yin musanya a fannin gine-ginen wasannin motsa jiki da kuma cibiyoyin horas da 'yan wasa ko kuma gabatar da wata kungiyar 'yan wasa ta hadin gwiwa da za ta iyar halartar wasannin kasa da kasa, misalin wasannin Olympic ko na Commonwealth.
Mista Badan Biscene, jami'in kula da harkokin hadin gwiwa a ma'aikatar wasannin motsa jiki ta Kamaru dake shugabantar tawagar kasarsa ya bayyana cewa, wannan muhimmin taro ne domin zai taimakawa kwararrun kasashen biyu wajen yin musanya a fannin wasannin motsa jiki. Amma babban makasudin wannan haduwa shi ne domin taimaka wa gwamnatocin kasashen biyu wajen bunkasa wasannin motsa jiki, in ji mista Biscene, kuma ya yaba wa Najeriya kan nasasar da ta samu a yayin gasar kwallon kafa ta duniya ta 'yan kasa da shekaru 17 da kungiyar kwallon kafa ta duniya FIFA ta shirya a kasar daular Larabawa da kuma nasararta a gasar cin kofin Afrika a Afrika ta Kudu a shekarar bara. (Maman Ada)