in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nahiyar Afrika na fatan samun lambobin yabo 35 a wasannin Olympic da za'a shirya a birnin London
2012-06-29 11:09:11 cri

Burin da nahiyar Afrika ta sanya a gabanta a wasannin Olympic na London da za'a shirya shi ne na samun lambobin yabo 35 tare da kusan goma sha biyar na zinari, in ji Hamad Kalkaba Malboum shugaban kungiyar guje-guje da tsalle-tsalle na Afrika a ranar Alhamis a Porto-Novo, babban birnin siyasar kasar Benin a yayin wata hirarsa da Xinhua. "'Yan wasan Afrika da suka halartar wasannin guje-guje na duniya karo na 13 da aka shirya daga ranar 27 ga watan Augusta zuwa 4 ga watan Satumban shekarar 2011 a Daegu, sun samu kyaututuka 30 wanda a ciki akwai kyautar zinari tara, goma na azurfa sannan sha daya na tagulla" a cewar mista Malboum. "A wasanni masu zuwa na Olympic, nahiyar Afrika tana fatan samun lambobin yabo a kalla 35 tare da fiye da na zinari goma sha biyar" Mista Hamad Kalkaba Malboum ya shaidawa Xinhua. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China