in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya yaba warware takaddamar kan iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru
2013-08-16 10:25:59 cri

A ranar Alhamis din nan, kwamitin sulhu na MDD ya yaba yadda Najeriya da Kamaru suka kammala harkokin mika ayyuka na tsibirin Bakassi, wato yanki mai arzikin mai da kasashen Najeriya da Kamaru suka yi takkadama a kai.

A cikin wata sanarwa, kwamitin ya yaba kokarin kasashen na nahiyar Afirka guda biyu kan yadda suka warware batun tsibirin Bakassi cikin lumana.

Tsibirin Bakassi yana nan ne a yankin Gulf na Guinea, wanda kuma kasashen biyu suka shafe shekaru suna takkadama kansa, wasu lokutan ma har da yin fada, har zuwa lokaci da suka amince da wani mataki da MDD ta bullo da shi a kan batun.

A shekarar 2002 ne kotun kasa da kasa (ICJ) ta warware batun bayan ta yanke hukunci a kai. Daga bisani yarjejeniyar Greentree ta biyo baya a shekarar 2006, wanda aka sa hannu kanta karkashin jagorancin tsohon magtakardan MDD Kofi Annan, inda kasar Najeriya ta amincewa bayar da iko ga kasar Kamaru kan tsibirin.

Kwamitin ya bukaci gwamnatocin Najeriya da Kamaru su inganta harkokin kulla aminci da za su kawo bunkasar batun tsaro da jin dadin jama'a da ayyukan shata kan iyakar. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China