Yawancin rumfunan zabe 22,263 dake cikin kasar sun kammala gaba dayansu domin taimakwa masu zabe yin rajista yadda ya kamata, in ji hukumar zaben.
Aikin na rajista na gudana cikin kwanciyar hankali a yawacin rumfunan zaben dake cikin wannan kasa, kuma fiye da kashi 99 cikin 100 na wadannan tashoshin zabe suna aiki yadda ya kamata tun lokacin da aka bude su da misalin karfe takwas na safe agogon wurin.
Hukumar zaben mai zaman kanta ta bayyana a ranar Jumma'a cewa, rajistan masu zabe game da zabubukan kasa da za'a shirya a shekarar 2014 a kasar Afrika ta Kudu za su gudana a ranaikun Asabar da Lahadi.
Kuma wadannan zabubuka na kasa da za su gudana a cikin shekara mai zuwa a wannan kasa za su taimaka wajen zaben sabuwar majalisar dokoki wadda ita kuma za ta zabi sabon shugaban kasa.
Kasar Afrika ta Kudu ita ce kasa ta farko a nahiyar Afrika a fannin tattalin arziki dake da yawan al'umma fiye da miliyan 53. (Maman Ada)