Ministan kula da harkokin 'yan sanda na kasar Afirka ta Kudu Nathi Mthethwa, ya bayyana a ranar Alhamis cewa, an samu raguwar aikata manyan laifuffuka a kasar a cikin shekaru 15.
Kamar yadda wani kamfanin da ke gudanar da bincike mai zaman kasa na kasar Amurka ya bayar da alkaluma da ke auwa mizanin aikata manyan laifuffuka (IHS) sun nuna cewa, yawan aikata manyan laifuffuka a kasar ta Afirka ta Kudu ya ragu matuka.
An kasa wadannan alkaluman ne gida biyu, wato alkaluman da suka shafi manyan laifuffuka kamar kisa da fyade da laifuffukan da suka shafi kadarori da shiga gidan mutane.
A cikin wata sanarwar da Mr. Mthethwa ya bayar, ya ce, aikata manyan laifuffuka a kasar, ya ragu da kimanin kashi 40 cikin 100 tsakanin shekarar 2002 da 2013, inda ya bayar da misali da alkaluman da IHS ya bayar, a bincike da ya gudanar a kasashe sama da 165 gami da sharhi mai zaman kansa.
Ministan ya ce, an samu raguwar kashi 24 cikin 100 na manyan laifuffukan da ake aikatawa a kasar da suka shafi kadarori a cikin wadannan lokuta da ake magana a kai.
Mr. Mthethwa ya ce, tun a shekarar 1994, kasar ta samu nasara wajen yaki da aikata manyan laifuffuka, inda a wannan lokaci aka samu karin hadin kan jama'a a yakin da ake da aikata manyan laifuffuka, ta hanyar mayar da hankali a wannan lokaci kan inganta rayuwar jama'a, musamman marasa karfi. (Ibrahim)