in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu ta kaddamar da katafariyar mahakar lu'u lu'u
2013-10-23 11:02:26 cri

Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu ya kaddamar da sabuwar mahakar ma'adanin lu'u lu'u, a wata sabuwar mahakar karkashin kasa dake Venetia, a arewa maso gabashin lardin Limpopo, mahakar da aka ce tana cikin irin ta mafi girma da kasar ta kaddamar a 'yan shakarun baya bayan nan.

Rahotanni sun bayyana cewa, aikin hakar lu'u lu'u a wannan sabuwar mahaka zai lashe jarin da yawansa ya kai kimanin dalar Amurka miliyan 200. Dama dai wannan yanki na Venetia shi ne yankin kasar da ya fi ko ina samar da ma'adanin na lu'u lu'u a dukkanin fadin kasar.

Da yake karin haske yayin bikin kaddamar da mahakar, shugaba Zuma ya ce, aikin hakar lu'u lu'u a wannan sabuwar mahaka ba karamin ci gaban da zai kawo ga tattalin arzikin kasar ba. Ya ce, da zarar an fara aikin cikin shekarar 2021, mahakar za ta rika samar da kimanin ma'aunin lu'u lu'u Carat miliyan 90 a tsahon shekaru 21.

Shugaba Zuma ya kara da cewa, sashen hakar ma'adanan kasar zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen raya arziki, da bunkasar kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China