in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Syria ba za ta tattauna tare da 'yan ta'adda ba
2013-10-21 10:10:05 cri

Ministan watsa labarai na kasar Syria Omran al-Zoubi ya jaddada cewa, kasarsa a shirye take ta halarci taron Geneva na biyu bisa sharudan da suka dace, amma duk da haka kuma ya nuna cewa, gwamnatin Syria ba za ta tattauna tare da 'yan ta'adda ba, a wani labari da kamfanin dillancin labarai na kasar SANA ya rawaito.

Tun farkon barkewar wannan rikicin kasar ne dai, gwamnatin Syria ta zargi wasu kasashen shiyyar da na yammacin duniya da tallafawa 'yan tawayen Syria, lamarin da ya mai da rikicin a wani yaki na bangarori daban daban da ya hada da gungun dakaru dake da alaka da kungiyar Al-Qaida wadda ke yaki da gwamnatin Syria.

Kalaman na ministan kasar Syria sun zo ne sa'o'i kadan bayan shugaban kungiyar tarayyar kasashen Larabawa Nabil al-Arabi ya bayyana cewa, taron na biyu kan batun zaman lafiya a kasar Syria zai gudana a birnin Geneva na kasar Swiss daga ranar 23 zuwa 24 ga watan Nuwamba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China