1020murtala dare.m4a
|
Tawagar farko dake kunshe da alhazan Najeriya 1000 za ta sauka dawo gida a ranar yau Lahadi 20 ga wata bayan kammala aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya.
Alhazan jihohin Kwara, Ogun, Osun da Oyo ne za su fara isowa a ranar yau din, wadanda tun farko su ne suka fara tashi zuwa kasar ta Saudiyya a ranar 14 ga watan Satumban da ya gabata.
Hukumar aikin hajji ta kasar Najeriya wato NAHCON ta tabbatar da cewa za'a kammala jigilar dawowar alhazan tare da kayayyakinsu cikin wata daya.
Alhazai dubu saba'in da biyar ne daga Najeriya suka sauke farali a shekarar bana, ciki har da dubu 10 wadanda suka je ta jirgin yawo. (Murtala)