Bisa labarin da aka samu, an ce, wannan rundunar sojin kasar da ke kunshe da sojoji fiye da 100 daya daga cikin rundunonin sojoji na farko da aka tura a kasar Mali. A ran 1 ga watan Agusta, Najeriya ta janye wadannan sojoji daga kasar Mali domin tura su zuwa jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar don yaki da mayakan kungiyar Boko-Haran. Sai dai wadannan sojoji ba su samu sauran albashinsu na aikin a kasar Mali , dalilin cewa rundunar sojan kasar ta Najeriya ta ci yawanci daga cikinsu.
Bisa tsarin albashi na aikin kiyaye zaman lafiya da MDD ta tsayar, an ce, ko wane sojan da ke kasar Mali zai samu albashi na dallar Amurka 1082 cikin ko wane wata daga MDD, watau tun lokacin da aka aike da wadannan sojoji zuwa kasar Mali a watan Janairu, har zuwa yanzu, bisa kididdigar da aka yi, gaba daya ko wane soja na da albashi sama da dallar Amurka 7000, amma har zuwa yanzu, kudin da ko wane soja ya samu ya kai kimanin dallar Amurka 5000, watau rundunar sojan kasar ta Najeriya ta lake sauran albashinsu. Bugu da kari, jami'in kula da harkokin bayar da albashi na rundunar sojan kasar bai ba da wani karin haske ba, kawai ya nuna cewa, ya bi umurnin shugabanninsa. (Maryam)