in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Alger ta tabbatar da sakin mutane uku da aka sace a kasar Mali
2012-07-16 15:00:59 cri
Ministan harkokin wajen kasar Algeria, Mourad Medelci ya tabbatar a ranar Lahadi a birnin Alger da labarin baya baya dake shaida sakin mutane uku daga cikin mutane bakwai da aka sace a arewacin kasar Mali.

"Jami'an diflomasiya an sake su kuma a yanzu haka suna kasar Algeria" in ji ministan a yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da takwaransa na kasar Faransa, Laurent Fabius dake kasar tun ranar Lahadi a wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu.

Sai dai kuma mista Medelci bai tabbatar da sakin sauran mutane hudu da ake garkuwa da su ba da suka rage.

Ministan ya maida martani ne kan wasu bayanai dake nuna cewa uku daga cikin jami'an diflomasiya 'yan kasar Algeria bakwai da aka sace a arewacin Mali an sake su kana an dawo da su ranar Talata ta jirgin sojojin kasar da ya sauka a filin saukar jiragen soja na Boufarik mai tazarar kilomita 45 dake kudu da birnin Alger.

A cewar kafofin yada labarai, gungun hadin kai da jihad a yammacin Afrika (Mujao) da ya dauki alhakin tsare jami'an diflomasiya na Algeria, kuma ya bayyana cewa yau da kusan sati guda ya saki uku daga cikin mutane bakwai da ya sace.

Karamin jakada na birnin Gao dake arewa maso gabashin Mali, tare da wasu jami'an diflomasiya shida an sace su a ranar biyar ga watan Afrilun da ya gabata a lokacin da birnin Gao ya fada cikin hannu masu fafatuka da makamai. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China