in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 20 sun rasu a sanadiyyar wani farmakin da aka kai wa wani masallaci a arewancin Nijeriya
2012-10-15 14:14:52 cri
A ran 14 ga wata, rundunar 'yan sanda a kasar Nijeriya ta bayyana cewa, mutane 20 ne suka rasa rayukansu, a sanadiyyar wani farmakin da aka kai wa wani masallacin dake jihar Kaduna, a arewancin kasar.

Bisa rahoton da rundunar ta 'yan sanda ta fitar, a wannan rana da sassafe, wasu mahara da ba a san ko su waye ba, sun shiga unguwar Dogon Dawa wadda ke da tazara da birnin Kaduna, kuma suka bude wuta kan fararen hula dake shirin koma gida bayan kammala salla, wanda sanadin hakan, mutane 20 suka rasa rayukansu.

Daga bisani kuma, wadannan mahara sun kai hari ga unguwar Birnin Gwari dake makwabtaka da Dogon Dawa, suka kuma kwashe dukiyoyi daga gidajen dake wurin, harin da ya sabbaba raunata wasu mutanen dake unguwar. Ya zuwa yanzu dai, ba a iya tabbatar da halin da garin ke ciki ba, musamman ma batun yawan mutanen da suka rasu ko suka jikkata, sakamakon wadannan hare-hare, wasu mutane sun tsira daga wurin daya bayan daya. Amma, rundunar 'yan sandan kasar ta riga ta fara gudanar da bincike kan lamarin.

Haka zalika ya zuwa yanzu, babu wata kungiya ko wani mutum da ya dauki alhakin gudanar da wannan farmaki. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China