in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tashar ba da taimako ga 'yan kasuwan nahiyar Afrika a birnin Guangzhou na kasar Sin
2013-10-24 17:45:54 cri

Birnin Guangzhou na kasar Sin ya kasance wuri da aka fi samun taruwan 'yan Afrika a kasar, a yankunan Yuexiu da Baiyun da sauransu, a kan gan su a ko ina. Wadannan 'yan Afrika sun yi doguwar tafiya zuwa nan kasar Sin ne don neman kyautata zaman rayuwarsu bisa taimakon bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin. 'Yan Afrika kimanin 1000 suna zama a unguwar Dengfeng na yankin Yuexiu, domin taimakawa musu cimma burinsu, ma'aikata a cibiyar ba da taimako ta unguwar sun yi kokari sosai. Masu sauraro, yanzu ga cikakken labari da abokiyar aikin mu Amina za ta karanto muku.

Da karfe biyar na yamma, a cikin ofishin ba da taimako ga 'yan kasashen waje na unguwar Dengfeng na yankin Yuexiu da ke birnin Guangzhou, wasu 'yan Afrika suna koyon Sinanci., wadanda yawacinsu suke gudanar da ayyukan ciniki a birnin Guangzhou.

"Da farkon fari, yawancinsu sun fito ne daga kasashn da suke yin amfani da Turanci, amma yanzu akwai dimbinsu da suke magana da Faransanci, hakan ya sa muka gayyaci masu sa kai da su koyar da su Sinanci"

Mataimakiyar farfesa kwalejin koyon ilmin kula da harkokin al'umma na jami'ar birnin Guangzhou Wang Liang ta jagoranci wannan ofishi. A cikin shekarar 2011, cibiyar ta gayyaci kungiya mai zaman kanta dake karkashen jagorancin Wang Liang da su taimaka ma 'yan Afirka dake zama a wannan unguwa. Wang Liang ta ce, muhimmin aiki da ake yi a yammacin ko wace rana shi ne koya wa 'yan Afirka Sinance, ta ce

"Suna bukatar koyon Sinanci. Wasunsu ko Turanci ma ba su ji ba, sai dai kawai Faransanci da Larabci, don haka da suka zo nan kasar Sin, su kan fuskanci matsala wajen yin mu'amala da sauran mutane."

Sakamakon matsalar da suke fuskanta ta fannin zaman rayuwa, wadannan 'yan Afrika na nuna himma da kwazo wajen koyon Sinanci, a cikin wannan ofishi mai fadin muraba'in mita 20, akwai mutane 40 zuwa 50 dake koyon Sinanci. Suleiman da ya zo daga kasar Guinea ya ce

"Sinawa da dama suna yin ciniki ko aiki a Guinea. Ina koyon Sinanci ne domin neman yin ciniki da su, saboda yawancin Sinawa ba su iya Faransanci, idan na iya Sinanci, to zan iya yin ciniki da su."

Koyon wani harshe yana daukan tsawon lokaci, kuma wadannan 'yan Afirka su kan fuskanci matsaloli ta fannonin kiwon lafiya da ba da ilmi ga yara da sauransu.

Wata yarinya mai suna Zhao Wenhua a cibiyar wadda ta kware a harshen Turanci, aikinta a ko wace rana shi ne ba da taimako ga 'yan Afrika domin warware matsalolinsu.

"Muna samar da taimakon jiyya ga matan Afrika da suka zo nan, sun zo sun yi tambaya ko muna iya bincike cutar Sida ko a'a. Sai na tuntubi asibiti da suke hadin kai da mu, kudi nawa ne za su kashe, hakan suna iya tsai da shirinsu."

Zhao Wenhua ta ce, cibiyar tana kuma shirya kwasa-kwasai a kai a kai da suka shafi harkokin shari'a da doka, tare da ba da taimako ga matan Afrika ta fannin binciken lafiyar jiki, da kuma taimakawa yaransu zuwa makaranta. Ban da haka, mu kan sanar da su kan abubuwa da dama, kamar su manufar shigi da fici, yin allurar rigakafi ga jarirai da sauransu.

A wata kusurwar ofishin, wasu yara suna wasa tare. Daga cikinsu, akwai wasu mai bakaken fata da suka fi jawo hankalin mutane.

"Ku kan zo wannan cibiya ko?"

"Haka ne"

"Me ku kan yi wasa da shi?"

"Computer"

"Kuna son wannan wuri ko?"

"Haka ne, kwarai"

"Saboda me?"

"Mutane na wannan wuri suna da kirki sosai."

Wannan yaro da ya iya Sinanci sosai sunansa shi ne Xiao Jiang, dan Congo Kinshasa ne, wanda ya zo nan birnin Guangzhou shekaru 4 da suka gabata, yanzu yana karatu a wata makaranta nan kusa da cibiyar. Saboda iyayensu na shan aiki, sai cibiyar ta zama gida ta biyu ga Xiao Jiang.

Cibiyar ta kan yi bukukuwa da dama, domin taimakawa 'yan Afirka da su yi mu'ammala da Sinawa, ta yadda za su yi mu'amala yadda ya kamata a nan kasar Sin cikin farin ciki. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China