Jiang Daming ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin na mai da muhimmancin sana'o'in dake da nasaba da ma'adinai ga ci gaban tattalin arzikin kasar. A 'yan shekarun baya, kasar Sin ta kammala ayyukan bincike da dudduba ma'adinai iri 25, ciki har da karafe-karafe, tagulla da dai makamatansu. Bugu da kari, ta gano wasu muhimman filayen adanar man fetur, man gas, kwal da fadin kowanensu yake da girma sosai. Sannan yawan ma'adinan da kasar Sin za ta iya samar a kowace shekara ya kai ton kusan biliyan 10 daga ton biliyan 6.8.
A lokacin da ake namijin kokarin farfado tattalin arzikin kasa da kasa, mr. Jiang Daming ya shawarci masu tafiyar da harkokin ma'adinan halittu da su yi hangen nesa su yi kokarin bunkasa sana'o'in ma'adinan halittu cikin hadin gwiwa. (Sanusi Chen)