in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Soyayyar Matasan Beijing' tana samun karbuwa a Najeriya
2013-10-20 17:12:41 cri

Ya zuwa yanzu, wasan kwaikwayon da aka fassara daga harshen Sinanci zuwa Hausa na Soyayyar Matasan Beijing, wanda aka shafe tsawon wata daya ana gabatar da shi ta kafar NTA HAUSA STARTIMES a kowace ranar Laraba da Asabar na samun karbuwa sosai. Domin neman sanin dalilin wannan farin jini na masu kallo wannan wasan kwaikwayo na Soyayyar Matasan Beijing? Wakilinmu Murtala dake Abuja ya hada mana cikakken rahoto.

Murtala: Abun da kuke saurara shi ne wasan kwaikwayon da Muhammed Baba Yahaya ya gabatar a wajen gagarumin bikin kaddamar da Soyayyar Matasan Beijing a Najeriya, wanda aka yi a ranar 18 ga watan Satumba a birnin Abuja. Tun lokacin da aka fara nuna shi ta NTA HAUSA STARTIMES, har zuwa yanzu, wannan wasan kwaikwayon kasar Sin cikin harshen Hausa ya samu babban yabo da karbuwa daga masu kallo.

Malam Usman Shehu Shagari, wanda ke zaune a Maraba, karamar hukumar Karu ta jihar Nassarawa ya ce yana sha'awar wasan Soyayyar Matasan Beijing kwarai da gaske, har ma ya gabatar da shi zuwa ga makwabtansa don su yi kallo tare.

Shi kuma a nasa bangaren, Malam Salisu Muhammed Dawanau, wani ma'aikacin gwamnati dake aiki a Abuja, babban birnin tarayya, ya bayyana ra'ayinsa game da wannan wasan kwaikwayo, har ma ya yabawa aiki tukuru da ma'aikatan sashen Hausa na CRI suka yi don fassara shi daga harshen Sinanci zuwa Hausa.

Baya ga yabo da kwarin-gwiwar da masu kallo suka bayar, akwai wasu masu kallo da suka gabatar da shawarwarinsu masu kyau ga wasan kwaikwayo na Soyayyar Matasan Beijing. Malam Muhammed Idi Gargajiga wanda ke zaune a jihar Gombe dake arewacin Najeriya yana fatan a wallafa faya-fayan bidiyo ko kuma DVD dangane da wasan a nan Najeriya.

Bugu da kari kuma, mukaddashin darekta mai kula da shirye-shirye na hukumar talabijin ta kasar Najeriya wato NTA malam Lawal Ahmed ya ce, ya zama dole a ci gaba da habaka hadin-gwiwa da mu'amala tsakanin hukumomin talabijin na Sin da Najeriya.

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China