John Kerry ya bayyan hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin masu sauraro, bayan jawabinsa ta kafar telibijin a gun taron da aka shirya a birnin London. Kerry ya ce, shi da shugaba Barack Obama sun samu cikkaken bayani don gane da wannan batu, kuma yanayin aikin tsaron kasar ne ya haifar da aukuwar hakan, sai dai duk da haka a cewarsa, aikin leken asiri na da muhimmanci wajen yaki da ta'addanci, wanda ya taimaka kwarai wajen murkushe makircin masu burin aiwatar da hare-haren ta'addanci.
A kokarin sanyaya ran abokan kasar ta Amurka daga kasashen Turai, mista Kerry ya ce, Amurka ta yi alkawarin ba za ta sake daukar irin wannan mataki ba a nan gaba.(Fatima)