A ranar Laraba 11 ga watan nan ne aka gudanar da bikin bude taron tattauna batutuwan da suka shafi tattalin arziki da akewa lakabi da Davos, a garin Dalian dake arewa maso gabashin kasar Sin.
Ana dai sa ran manyan 'yan kasuwa, da jami'an gwamnatoci, da masana da yawansu ya kai 1500 daga kasashe kimanin 90 za su halarci taron na yini uku, za kuma su tattauna kan hanyoyin wanzar da ci gaba, da inganta samar da makamashi, da kuma batun cinikayya da zuba jari.
Da yake gabatar da jawabin bude taron na bana, wanda a kaiwa lakabi da 'cimma muhimmin burin kirkire-kirkire', firimiyan kasar Sin Li Keqiang, ya ce, gudanar da sauye-sauye, da kirkire-kirkire su ne ke ba da damar samun ci gaba.
Li ya kara da cewa, tun farkon shekarar nan ta bana, kasar Sin ke samun nasarori wajen aiwatar da manufofin ci gaba, da tabbatar da daidaito, tare da gudanar da sauye-sauye masu ma'ana, nasarorin da a cewarsa sun samu ne sakamakon bunkasa tsarin tattalin arziki daga dukkanin fannoni, da kuma amfani da ingantattun fasahohi ci gaba.
Da yake tsokaci kan batun matsalolin da tattalin arzikin duniya ke fuskanta, firimiyan na kasar Sin ya ce, kasarsa za ta kai ga samun kaso 7.5 bisa dari na ci gaba a fannin tattalin arziki, duk kuwa da tarin kalubalen da tattalin arzikin duniya ke fuskanta.
Daga nan sai ya yi kira ga daukacin kasashen duniya da su dauki matakan da suka dace wajen ganin sun bude kofofinsu ga ragowar kasashe, su kuma yi watsi da tsarin sanya shinge ga huldodin ciniyayya. Don gane da hakan ne ma Li ya ce, kasar Sin, ta dauki aniyar yin hadin gwiwa da ragowar kasashen duniya wajen musayar kwarewa, tare da ba da taimako ga kasashe masu tasowa, da ma uwa uba ta hanyar daukar duk wani mataki da zai samar da ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya. (Saminu)