in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firimiyan Sin ya yi kira da a amince da ikon kasashe masu tasowa na bunkasa tattalin arziki
2013-09-10 16:17:08 cri

Firimiyan kasar Sin Li Keqiang, ya yi kira ga kasashen duniya da su amince da ikon da kasashe masu tasowa ke da shi na iya bunkasa tattalin arzikinsu, tare kuma da shawo kan irin kalubalan da fannin tattalin arzikinsu ke ciki a halin yanzu, duk kuwa da jan aiki dake tattare da hakan.

Li wanda ya bayyana hakan ranar Litinin yayin zantawarsa da shugaban dandalin tattalin arziki na duniya ko WEF a takaice Klaus Schwab, a garin Dalian dake arewa maso gabashin kasar Sin.

Firimiyan kasar ta Sin wanda ya tattauna da Schwab gabanin bude taron tattalin arziki da ake wa lakabi da Davos, ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da daukar dukkanin matakai da za su habaka tattalin arziki, da inganta rayuwar al'umma, tare da karfafa hadin gwiwa tsakaninta da ragowar kasashen duniya.

Da yake tsokaci don gane da batun kasar Syria ko Sham kuwa, Li ya ce, wajibi ne kasashen duniya su girmama matsayin MDD, su kuma yi kokarin shawo kan matsalar kasar ta hanyar siyasa. Ya ce, a bangaranta kasar Sin za ta ba da dukkanin goyon baya, wajen samar da yanayin daidaito, zaman lafiya da kwanciyar hankali a sassan duniya.

A nasa jawabi, Klaus Schwab, ya ce, gudanar da taron Davos na wannan karo a kasar Sin ya dace kwarai, musamman ganin irin rawar da kasar ke takawa a fannin tattalin arzikin duniya tsahon shekaru 42 da shigarta dandalin WEF.

Ana sa ran firimiyan kasar ta Sin Li Keqiang, zai halarci taron na Davos na wannan shekara, da za a bude ranar 11 ga watan Satumbar nan, ya kuma gabatar da bayani gaban mahalartansa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China