Bisa labarin da aka samu, an ce a farkon watan Satumbar wannan shekara ne, wadannan 'yan ci rani suka tashi tashe daga birnin Arlit da ke da nisan kilomita 150 daga yankin iyakar Niger da Algeria, suka keta cikin hamadar da ke tsakanin kasashen biyu, domin kaucewa tashoshin binciken jami'an tsaro. Amma, sakamakon lalacewar motocinsu guda biyu, dukkansu suka rasa rayukansu cikin hamada, ciki hada da mata 32, da yara kanana 48. Bugu da kari, bisa bayanin da kasar Niger ta bayar, an ce, da ma dai rundunar sojan kasar ta taba gano gawawwaki guda 5 a wannan yanki, wadanda su ma 'yan ci rani ne. (Maryam)