Shugaban ya bayyana hakan ne a birnin Niamey lokacin da yake bude taron karawa juna sani na masu ruwa da tsaki a harkokin shari'a, wanda ma'aikatar shari'a ta kasar ta shirya.
Manufar taron wanda sama da mahalarta 500 da ke wakiltar kwararru kan doka da sauran kwararrun bangarorin da suka shafi jin dadin jama'a a kasar ke halartar, ita ce yi wa bangaren shari'ar kasar da cin hanci ya yi wa katutu gyaran fuska.
Shugaban ya bukaci mahalarta taron, da su fito da dabarun da za su taimaka wajen maido da martabar sashen na shari'a, ta yadda alkalai za su rage karbar na goro tare da yanke hukunci bisa gaskiya da adalci.
Bugu da kari Shugaba Issoufou ya yi kira da a yi musayar ra'ayoyi game da muhawarorin da a kullum bangaren shari'ar kasar ke gabatarwa, matakin da ya dakushe martabar sashen kana ya shafi aikinsa.
Duk da koma bayan sashen na shari'a, shugaban na Niger ya sake nanata kudurinsa na ganin an nuna ba sani ba sabo wajen yanke hukunci a kasar ta Niger.(Ibrahim)