in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hako mai da wani kamfani na Nijeriya
2012-11-02 20:43:27 cri
Ministan albarkatun mai a Jamhuriyar Nijar Foumakoye Gado ya saka hannu a kan wata yarjejeniyar bincike tare da hako albarkatun mai da wani kamfani na kasar Nijeriya Sirius Energy Resources. Yarjejeniyar ta ba da dama ga kamfanin wajen hako albarkatun mai a rijiyar Gerin wanda ke arewa maso yammacin rijiyoyin mai na Agadem, kamar yadda wata majiya daga ma’aikatar makamashi ta Nijar ta sanar a jiya Alhamis, wanda ta yi bayanin cewa, wannan yarjejeniya ta kuma bai ma wannan kamfanin damar nemo man kocokan a wannan rijiya ta Gerin har na wa’adin shekaru hudu. Sakamakon wannan saka hannu, kamfanin na kasar Nijeriya zai biya gwamnatin kasar Nijar rarar kudi kimanin dalar Amurka miliyan biyar. Yana kuma da alhakin binciko tare da hako man domin nuna yiyuwar samar da mai daga wannan rijiya. Wannan shi ne karo na biyu da kasar Nijar ke rattaba hannu a kan irin wannan yarjejeniya bayan da ta saka hannu kan yarjejeniya da wata kamfanin ta kasar Sin a shekara ta 2008, wanda ya yi sanadiyar gano albarkatun man mai dimbin yawa a rijiyoyin Agadem. A cewar wannan majiya, har ila yau, kwannan nan za’a sake saka hannu kan wasu yarjeniyoyi da wasu kamfanonin a wannan fanni domin inganta bincike da kuma hako man a kasar Nijar.(Fatimah Jibril)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China