A cikin sakon murna, Mohamed Bazoum ya furta cewa, "Ka zama babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a gun babban taron wakilan JKS karo na 18 da aka kammala ba da dadewa ba, tare da daukar babban nauyin dake kanka na ci gaba da bunkasa babbar nasarar da JKS ta samu cikin shekaru sama da 90 da suka wuce. A madadin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PNDS da kuma dukkan 'yan jam'iyyar, ina fatan kai da ma duk sauran membobin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin za ku yi nasara wajen tafiyar da dukkan kudurorin da aka zartas a wannan babban taro. Na yi imani cewa, a karkashin jagorancinka, kasar Sin za ta kara samun ci gaba, tare da taka muhimmiyar rawa wajen ci gaba da sa kaimi ga kafa wata duniya mai zaman lafiya da hadin kai da jituwa da kuma wadata."(Fatima)